Rayuwar Daliba a kasar Turkiyya: Ruqayya Sadauki

Za ku iya sauraron tattaunawa da mu kai da Ruqayyat Saduaki.

TARIHI NA

Kamar yadda na fada sunana Rukayyat. Ni haifaffiyar garin Suleja ce a Jihar Neja, Babana Dan Katsina ne,  Mamata ‘Yar Jihar Neja ce.  Na yi karatun firamare har zuwa sakandare duk a Jihar Neja.  Bayan na gama Sakandare ne Babana ya nema min babbar makanta a Katsina, wato Hassan Usman Katsina Polytechnic, a shekarar 2013 na fara karatun share fagen Difiloma, inda na karanchi Home Hospitality (Nazarin Tsara Jindadin Zaman Gida) na shekara daya.  Bayan na gama, na nemi canjin kwas zuwa karatun jarida, wato journalism inda na karanchi mass communication a matakin Difiloma ta kasa. Bayan na gama ne cikin ikon Allah na samu aiki da Jaridar LEADERSHIP Hausa da ta Turanci, İnda na yi aiki dasu na shekara daya.

Na yi rubuce-rubuce sosai a lokacin kamar a kan “women gender ekuality (Daidaiton Jinsin Mata)” “Effect of prostitution (Illar Karuwanci)” da kuma wani shafi nawa na kaina da nake yi wato “kiddies story (filin yara)” wanda ke fitowa a kowace Talata. Ina cikin aiki da Turanci ne kuma na fara aiki da Sashen Hausa duk a LEADERSHIP din na dan lokaci, kafin na bari lokacin Al’amin Ciroma shi ne Draktan Sashen Hausa, a cikin wannan kankanin lokacin na fara aiki da Gidan Talabjin na Farin Wata inda ake gayyatata lokuta-lokuta muna tattaunawa a wani shiri mai suna Muharawa, inda shirin da na fara shiga shi ne “TsakaninRubutu da Hoto a jarida, wanne ya fi amfani?”. 

RAYUWA A KASAR TURKIYYA

Toh, yadda kowace kasa da yadda take da tsari na karatu, haka su ma anan din, wasu abubuwan sun bambanta. A zahirin gaskiya karatu a kasar Turkiya kamar sun fi ba da muhimmanci a kan koyon karatu a aikace, kuma karatun ba a takure ake yin shi ba, koda dai da wahala karatun saboda a kullum ba a barin aji sai da assignment (Jinga) da sauransu. Kuma a nan gaskiya babu batun yajin aikin malaman makaranta, ba’a yi. Kuma ana bawa mutum damar idan ya fadi jarabawar farko ya kara maimatawa a wannan lokacin wanda ake kira ‘makeup edam’. Haka nan karatuna na journalism (aikin jarida) a Turkiya ya min sauki kuma ba komai ba ne ya sa hakan illa lokacin da ina Katsina Polytechnic na koyi abubuwa da yawa a fanin jarida, kamar fannin aikin a aikace da gudanar da bincke, ina alfahari da makarantar wato HUK Polytechnic. Shi yasa ko a nan da na zo suna mamakin kwazona da yadda nake gane duk wani abu da ake koyarwa a karamin lokaci, a yanzu haka ina tafiya da 3.55GP ne, ina fatan na zamo abin alfahari ga kasata, iyayena da malamaina da abokan arziki.

Ba Ina nufin karatu a Nijeriya ya fi sauki ba ne ba, ya danganta da yadda ka fara karatun. Kamar ni kin ga sai da na karanci ‘mass communication’ a nan Nijeriya, da na gama kuma na yi aiki da gidan talabijin da gidan jarida, So (don haka) ina da edperience (basira) na wasu abubawa theory aspect (dunkulallen nazari) har da pratical aspect (karatu a aikace). Shi ya sa karatun yai min sauki saboda wasu abubuwan da ake koya mana wasu na riga na sansu. Gaskiya karatu a Turkey idan mutum ba mai san karatu ba ne ba zai iya ba, saboda karatun suke koyarwa sosai a kan abin da kake karanta, suna san research works (bincike-bincike) sosai wanda ba kowane dalibi ke son haka ba, saboda yana da daukar lokaci kuma yana bukatar bincike mai zurfi a kan abin da aka baka ka nemo. So (don haka) a ko ina a tunanina idan kana son abu duk wahalarsa za ka yi iya kokarinka ka yi shi dan ka cinma burinka.