Bani da shi, ya ya zan yi? {Hausa}

 

Jinkiri yana zuwa mana ta hanyoyi da ban da ban, za ka ga kana so ka yi abu, amma sai ka rinka jinkirtawa, har wani sa’in ya wuce ma ba ka samu ka yi abun da ka ke so ba. Misali, kana so ka fara gini, ko ka yi wani abu na musamman wanda za ka samu nasara, sai dai ka rinka ba wa kanka uzuri cewa idan na samu kaza zan fara, ko kuma idan kaza ya faru, zan fara. ire iren uzururukan nan ke jawo rashin ci gaba a rayuwa.

So da yawa mu na jinkirta abubuwa saboda wani uzuri da muke ba wa kan mu domin kada muyi abun da mu ka saka a gaba. Misali, kasuwanci muke so mu fara, sa dai mu ce ai sai mun samu lokaci, ko kuma sai mun samu wasu kudade, ire iren uzururukan nan mu ke ba wa kan mu, kuma mu ke hana kan mu ci gaba. Wannan bidiyo ya ba da matakai guda uku da mutum zai iya bi, ya wuce wannan uzurai har ya fara abun da ya saka a gaba.